in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin Duniya: za a samu farfadowar tattalin arziki a fadin duniya
2018-01-10 20:46:07 cri
Jiya Talata ne, bankin duniya ya daidaita hasashen da ya yi game da makomar tattalin arzikin duniya a bana da shekara mai zuwa, yana ganin cewa, za a samu farfadowar tattalin arzikin duniya a shekarar 2018 a duk fannoni tun bayan da duniya ta gamu da matsalar kudi, kana kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen inganta karuwar tattalin arzikin duniya.

Bankin duniya ya yi hasashen cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin ta kai kashi 6.8 cikin dari a shekarar 2017, wato karuwar kashi 0.3 bisa kan hasashen da ya yi a watan Yunin bara. A shekarar 2018 kuma, karuwar za ta kai kashi 6.4 cikin dari, wato karuwar kaso 0.1 bisa hasashen bara. A shekarar 2019, tattalin arzikin kasar ta Sin zai karu da kashi 6.3 cikin dari, wanda ya yi daidai da hasashen da ya yi a watan Yunin bara. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China