in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen zuba jari a kasashe masu tasowa
2017-10-11 10:23:55 cri
Yayin da kara takure manufofin da suka shafi harkokin kudi zai kara matsa lamba kan kimar kayyyaki ko kadarori a kasashe maso tasowa, jarin kasar Sin zai taimaka wajen rage barazanar a kasashen.

Rahoton da kamfanin Moody mai nazarin harkokin kudi ya fitar a jiya Litinin, ya bayyana kasashen a matsayin wadanda ba su da yawan hannayen jari, kuma suka dogara kan jari kalilan da suke samu, inda ya bayyana kasashe 36 da suka shiga suka fada rukunin.

Rahoton ya ce kasashen su ne wadanda suka dogara a kan shigar da kayayyaki daga wasu kasashe da rashin isasshen tsarin harkokin kudi da kuma yawan bukatar bashi.

A cewar rahoton, matsalar za ta fi shafar kasashen Masar da Pakistan da Mongolia.

Ya kara da cewa, zuba jari kai tsaye na kasar Sin ya zama wani muhimmin abu ga wadancan kasashe, inda 16 daga ciki suka kasance karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya" na kasar Sin.

Kamfanin Moody ya ce jarin kasar Sin zai taimaka wajen magance hadarin da za a iya fuskanta a nan kusa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China