Wannan hasashe dai ya dara na watan Yunin bara da kaso 0.2 bisa dari, kamar dai yadda hakan ke kunshe cikin rahoton wani asusun bada lamuni mai hedkwata a birnin Washington.
Kaza lika rahoton asusun ya nuna cewa, a shekarar ta bana, akwai alamun samun habakar tattalin arzikin duniya cikin kyakkyawan yanayi, kusan irin sa na farko tun bayan tsundumar da duniya ta yi cikin halin matsin tattalin arziki.
A bara an yi hasashen samun ci gaban tattalin arziki da kaso 3 bisa dari, wanda shi ne mafi gamsarwa da aka samu tun fara farfadowar tattalin arzikin duniya a shekarar 2011, bayan da aka samu kaso 2.4 bisa dari a shekarar 2016.
A wani bangaren kuma, rahoton ya ce ci gaban tattalin arzikin da aka samu a 2017 ya shafi sassan duniya da dama. Sai dai kuma bankin duniyar ya yi kashedin cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin ana ci gaba da fuskantar matse bakin aljihu a hada hadar kudade tsakanin kasashen duniya, da fadadar wasu takunkumi, da kuma rashin jituwa ta fuskar siyasa dake karuwa tsakanin wasu yankunan duniya.(Saminu)