A jawabin sa yayin bikin bude taron, Song Tao ya bayyana cewa, dunkulewar kasar Sin da kasashen Afirka tana da muhimmanci ga dunkulewar kasa da kasa, kuma bayan da aka yi taron wakilan JKS karo na 18, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya ci gaba da samun bunkasuwa bisa fannoni daban daban, kuma cikin kyakkyawan yanayi. Kaza lika a matsayin wani muhimmin bangare na tsara manufofin wata kasa, jam'iyyun siyasa sun yi babban tasiri kan bunkasuwar kasa da kasa, da kuma dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu.
Ya kuma kara da cewa, bayan shiga sabon zamani, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta dukufa wajen yin mu'amala da jam'iyyun kasa da kasa, domin karfafa dunkulewar kasar Sin da kasashen Afirka, da zurfafa fahimtar juna a tsakaninsu a fannin siyasa da kuma karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata, ta yadda za a karfafa dunkulewar kasa da kasa baki daya. (Maryam)