Wannan taro ya samu halartar wasu kwararru da masana sama da dari daga kasar Sin da kasashen Afirka guda tara, ciki har da Najeriya, da Habasha, da Afirka ta Kudu da sauransu. Cikin masanan da suka zo daga Najeriya, akwai shehun malami Gambo Babandi Gumel daga jami'ar tarayyar dake birnin Dutsen jihar Jigawa, da malam Kabiru Adamu Kiyawa, manajan bankin Zenith reshen birnin Dutsen.
A jawabin da ta gabatar a yayin taron, Dokta Beatrice Njenga, babbar jami'a a sashin kula da harkokin daukar ma'aikata da kimiyya da fasaha na hukumar kungiyar tarayyar Afirka, ta ce, irin nasarorin da kasar Sin ta samu a fannonin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al'umma sun zama abubuwan koyi ga kasashen Afirka. Tana fatan wannan taro zai zama wani muhimmin dandali ga Sin da Afirka domin yin musanyar ra'ayi dangane da habaka hadin-gwiwa da karfafa dankon zumunci.
Ita ma a nata bangaren, shugabar jami'ar horas da malamai a fannin fasahohi ta Tianjin, Madam Liu Xin ta bayyana cewa, habaka hadin-gwiwa a fannin masana'antu tsakanin Sin da kasashen Afirka, wani muhimmin sashi ne na shawarar 'ziri daya da hanya daya' da kasar Sin ta bullo da ita. Madam Liu tana fatan al'ummomin Sin da Afirka za su alfana da wannan hadin-gwiwa.(Murtala Zhang)