in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar PLO ta dakatar da amincewa da kasar Isra'ila
2018-01-17 11:07:41 cri

A daren ranar 15 ga wata ne, aka rufe taro na 28 na babbar hukumar kungiyar kwatar 'yancin Falasdinu(PLO), inda aka bayar da wata sanarwa, wadda ta bayyana sabon matsayin da Falesitnu ta dauka kan kasashen Amurka da Isra'ila, da kuma yunkurin shimfida zaman lafiya tsakanin Falasdnu da Isra'ila, kana da sanar da dakatar da amincewa da Isra'ila.

An shirya wannan taron gaggauwa na kwanaki biyu ne bisa bukatun shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, bisa taken "Kudus babban birnin kasar Falasdinu har abada".

Shugaban hukumar Falasdinawa, kana shugaban kungiyar kwatar 'yancin Falasdinu wato PLO a takaice Salim Zanoun shi ne ya karanta sanarwar a yayin bikin rufe taron. Game da batun dangantakar dake tsakanin Falasdinu da Amurka, sanarwar ta la'anci da kuma kin amincewa da kudurin da shugaban Amurka Donald Trump ya tsaida a farkon watan da ya gabata na amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, da mayar da ofishin jakadancin kasar Amurka zuwa birnin Kudus daga birnin Tel Aviv. Sanarwar ta ce, kasar Amurka ta kasa zama mai shiga tsakani kan yunkurin shimfida zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra'ila. Sai Amurka ta soke wannan kudurin game da birnin Kudus, kafin ta kasance mai shiga tsakani a wannan yunkuri.

Game da dangantakar dake tsakanin Falasdinu da Isra'ila ma, sanarwar ta nuna cewa, saboda Isra'ila ta dakatar da yarjejeniyar da ta sanyawa hannu tare da Falasdinu, don haka, babbar hukumar PLO ta jaddada cewa, za ta yi kokarin tabbatar da 'yancin kasar Falasdinu, za a kafa wata kasar Falasdinu mai 'yancin kai, bisa yarjejeniyar iyakar kasa da aka shata a shekarar 1967, kana birnin gabashin Kudus a matsayin babban birnin ta. Sanarwar ta dankawa hukumar zartaswar kungiyar PLO iznin dakatar da amincewa da Isra'ila, har zuwa lokacin da Isra'ila ta amince da kasar Falasdinu mai iyakar kasa da aka shata a shekarar 1967, da soke kudurin mamaye gabashin Kudus, da kuma dakatar da gina matsugunan Yahudawa. Kana babbar hukumar ta sake nanata dakatar da duk wasu ayyuka da Isra'ila. Baya ga haka, sanarwar ta jaddada cewa, matsugunan Yahudawa da Isra'ila ta gina a farkon shekarar 1967 sun sabawa doka, Falasdinu za ta ci gaba da hada kai da sauran kasashe daban daban don nuna adawa da yadda mahukuntan Isra'ila ke gina matsugunin Yahudawa bisa ra'ayin mulkin mallaka. Haka zalika, Falasdinu za ta kara nuna adawa da Is'raila, da ma janye kudaden da ake zubawa a Isra'ila, ta kuma yi kira ga kasashe daban daban da su sanyawa Isra'ila takunkumi, da nufin dakatar da ayyukanta da suka sabawa dokar kasa da kasa, tare kuma da hana kai hari da take yi kan Falasdinawa, da yadda take nunawa Falasdinawa wariya

Ban da wannan kuma, sanarwar ta ce, Falasdinu za ta zartas da kudurorin da aka tsaida a tarukan koli na kawancen kasashen Larabawa game da batun Kudus, musamman ma kudurin da aka zartas a taron kolin kawacen da aka shirya a shekarar 1980 a Amman, babban birnin kasar Jordan. Kudurin da ya bukaci a yanke hulda da duk kasashen da suka amince da mayar da Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, da ma batun mayar da ofishin jakadancinsu dake Isra'ila zuwa Kudus.

A cikin sanarwar, shugaban hukumar Falastinawa, kuma shugaban kungiyar PLO Salim Zanoun ya bayyana cewa, bisa yanayin da ake ciki, akwai bukatar ganin an gaggauta samun sulhu, da kawo karshen baraka a cikin Falasdinawa. Baya ga haka, ya bayyana cewa, za a shirya taron hukumar Falasdinawa, inda za a gayyaci kungiyar Hamas da ta Jihad, da nufin zaben sabuwar hukumar Falasdinawa. Kungiyoyin biyu ba su halarci wannan taron na babbar hukumar PLO ba.

A watan Maris na shekarar 1977, a yayin taro karo na 13 na hukumar Falasdinawa, wato babbar hukumar kungiyar PLO, an tsaida kudurin kafa babbar hukumar kungiyar, wadda shugaban hukumar Falasdinawa ya zama shugabanta, mambobinta sun kunshi mambobin hukumar zartaswa ta kungiyar, da wakilan jam'iyyu da kungiyoyi daban daban.

A ranar 6 ga watan da ya gabata ne, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da amincewa da Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila, kana ya ba da umarnin mayar da ofishin jakadancin Amurka dake Isra'ila daga Tel Aviv zuwa Kudus. Daga baya, Falasdinu ta sanar da cewa, kasar Amurka ba ta cancanci zama mai shiga tsakani a yunkurin shimfida zaman lafiyar Falasdinu da Isra'ila ba. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China