Guterres wanda ya bayyana hakan ga zaman kwamitin sulhun majalisar, ya ce wajibi ne a hana aukuwar tashin hankali, maimakon a magance shi bayan tashin sa.
Jami'in na MDD ya kara da cewa, hana aukuwar tashin hankali zai rage kuncin da jama'a za su shiga da ma makuden kudaden da za a kashe a kokarin kwantar da wutar tashin hankalin. Ko da yake ba kowa ne zai fahimci hakan ba, amma rigakafi ya fi magani.
Ya ce, ajandar nan ta bunkasuwa nan da 2030 ta zayyana dukkan muhimman matakai da damammaki na hana aukuwar rikici. Sauran sun hada da raya kasashe, mutunta daukacin bil-Adama, inganta rayuwar jama'a da batun al'adu.
Guterres ya ce, batun daidaiton jinsi yana da alaka da jurjurcewa, an kuma samu nasara wajen damawa da mata daga batun hana tashin hankali zuwa ga batun tabbatar da zaman lafiya. Ya ce yanzu haka ,ana damawa da mata a harkokin yau da kullum. (Ibrahim)