in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban sakataren MDD ya jaddada muhimmancin hadin kai
2018-01-01 12:20:36 cri

A ranar farko ga watan Janairun shekarar 2018, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya gabatar da wani jawabi na taya al'ummar kasa da kasa murnar shiga sabuwar shekara, kana kuma, ya nuna cewa, yanzu haka ana fuskantar kalubaloli da dama a duk fadin duniya.

Mr. Guterres ya jaddada cewa, hadin kai, hanya ce da wajibi ne a bi ta domin daidaita wadannan kalubaloli.

Mista Guterres ya ce, "a ranar farko ta wannan shekara, ina kira da a hada gwiwa. Na yi imani da cewa, za mu iya kara samun tsaro a duniyarmu. Za mu iya magance rikici, da zub da jinin juna, da kiyaye ra'ayinmu na bai daya, amma ba za mu iya yin haka ba, har sai mun hada kanmu sosai. Na kalubalanci shugabanin kasa da kasa da su mayar da "rage gibin da ke tsakaninmu, da kawar da sabani, da cimma ra'ayi daya, da sake amincewa da juna, a matsayin burinsu na sabuwar shekara. Hadin kai, hanya ce da wajibi ne mu bi. Muna dogaro da hadin kai domin samun makoma mai kyau, a kalaman Mr. Guterres." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China