A yau ne kasashen Koriya ta kudu da na Arewa suka amince su gudanar da wata tattaunawa kan harkokin da suka shafi soja, bayan wata ganawa da manyan jami'an kasashen biyu suka gudanar a Panmunjom dake yankin da aka haramta ayyukan soja tsakanin kasashen biyu.
Wata sanarwar hadin gwiwa da aka rabawa manema labarai bayan tattaunawar, ta bayyana cewa, Koriya ta arewar ta kuma amince ta tura wata tawaga zuwa gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi da kasar Koriya ta kudu za ta karbi bakunci a wata mai kamawa.