in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AIIB ya kara yawan mambobi
2017-03-24 12:54:25 cri
Bankin zuba jari don gina kayayyakin more rayuwa na nahiyar Asiya (AIIB) ya sanar a jiya Alhamis cewa, hukumar gudanarwarsa ta amince da sabbin bukatu 13 da aka gabatar mata na neman zama mambobin bankin.

Wannan shi ne karon farko da bankin ya samu karin sabbin mambobi tun bayan kafa shi a shekarar 2015, kuma da wadannan sabbin mambobi a yanzu haka adadin mambobin na AIIB ya kai 70.

Sabbin mambobin da aka amince da su sun shafi na shiyyoyi 5, wadanda suka hada da Afghanistan, Armenia, Fiji, Hong Kong ta kasar Sin da Timor Leste, sauran 8 wadanda ba na shiyyar ba su ne: Belgium, Canada, Ethiopia, Hungary, Ireland, Peru, Sudan da Venezuela.

Shugaban bankin na AIIB Jin Liqun, yace karuwar masu sha'awar shiga gayyamar bankin ta nuna a fili yadda ake samun ci gaba wajen raya bankin ya zama na kasa da kasa.

Yace yana matukar alfahari kasancewar AIIB yana da mambobi daga kusan dukkan nahiyoyi na duniya, kuma ana fatan samun karin sabbin mambobi a cikin wannan shekara.

AIIB mai hedkwata a Beijing, an kafa shi ne da nufin bunkasa tattalin arziki da raya cigaban nahiyar Asiya wajen samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa da suka dace da yanayin bukatun jama'a.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China