in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya da bankin AIIB sun zurfafa hadin gwiwarsu
2017-04-24 11:01:06 cri
Bankin duniya da bankin zuba jari ga aikin gina kayayyakin more rayuwa a nahiyar Asiya (AIIB), sun kulla wata yarjejeniya a birnin Washington na kasar Amurka a jiya Lahadi, da nufin zurfafa hadin gwiwa tsakanin su.

Bankin duniya ya ba da sanarwa a jiya cewa, yarjejeniyar da aka kulla ta shata wani tsari ne ga aikin hadin kai tsakanin bankunan 2, musamman ma a fannonin tara kudi, da musayar ma'aikata, da dai sauran batutuwan dake janyo hankalin bankunan, ta yadda za a aza harsashi mai kyau na hadin gwiwar bangarorin 2, a matakin shiyyoyi da kasashe.

Cikin sanarwar bankin duniyar, shugaban bankin mista Kim Yong ya bayyana cewa, tun bayan da aka kaddamar da bankin AIIB, bankin duniya ya fara hadin kai tare da shi. A cewarsa, hadin gwiwa a tsakanin hukumomin raya kasa na da muhimmanci sosai, musamman ma a fannonin janyo hankalin sassa masu zaman kansu, da biyan bukatun samun ci gaba.

A dai wannan sanarwa, Jin Liqun, dake shugabantar bankin na AIIB, ya ce, kulla yarjejeniyar ya dace da akidar bankin AIIB game da hulda da karin kasashe, kuma ya zurfafa huldar hadin kai dake tsakanin bankunan 2. Ya ce yana sa ran ganin samun sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar, musamman ma a yankin Asiya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China