Costantinos Bt. Costantinos, wanda jami'i ne mai bada shawara kan harkokin tattalin arziki na kungiyar tarayyar Afrika da hukumar gudanar da tattalin arzikin Afrika ta MDD, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, nan gaba kadan kasashen Afrika zasu bi sahun kasashen Afrika ta kudu, da Masar da Habasha wajen shiga shirin na AIIB.
Yace shirin wata babbar dama ce wanda zata samarwa kasashen cigaban ababen more rayuwa.
Costantinos, wanda kuma shehun malami ne a sashen nazarin dabarun jin dadin al'umma a jami'ar Addis Ababa yace, sakamakon zama mamba a shirin na hadin gwiwa da hukumomin samar da kudade wanda kasar Sin ta bullo dashi, a halin yanzu kasashen Habasha da sauran kasashen Afrika zasu iya samun damar karbar rancen kudade da samun tallafin ayyukan gina ababan more rayuwa.
A cewarsa, cigaban kayayyakin more rayuwa, da cigaban raya birane, da samar da gidaje, da masana'antu, da bunkasa aikin gona, da gina cigaban bil adama na daga cikin bangarorin da kasashen na Afrika zasu ci gajiya idan suka kasance mamba a AIIB.