in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Shigar da kasar Amurka a AIIB ba wani abu ne maras kyau ba
2016-11-15 18:50:25 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya ce, bankin zuba jari na Asiya wato AIIB a takaice hukuma ce da ta kunshi bangarori da dama. A fannin karbar sabbin mambobi kasar Sin ba za ta yi magana a madadin bankin da sauran kasashe mambobi ba. Amma, a ganin kasar Sin, idan kasar Amurka wadda ke zama kasa mafi girman tattalin arziki tana son shiga bankin, wannan ba laifi ba ne.

Mr. Geng ya bayyana hakan ne yau Talata a yayin taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing.

Rahotanni na cewa, mai ba da shawara ga shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya taba bayyana cewa, rashin shigar kasar Amurka bankin AIIB babban kuskure ne. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China