Jami'in na Sin wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan ganawarsa da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Masar mai kula da harkokin kasashen Larabawa Tarek Al-Kouni. Ya ce sun fahimce wasu kasashe sun canza matsayinsu game da batun Syria, wannan wata kyakkyawar dama ce ta warware batun ta hanyar siyasa.
Xie ya ce, matakan da masu ruwa da tsaki a wannan batu suka dauka na amincewa su kafa shiyoyin tsaro, alama ce dake nuna cewa, al'ummomin kasa da kasa suna fatan bangarorin da wannan rikici ya shafa, za su yi kokarin warware bambance-bambance dake tsakaninsu, ta yadda za su hanzarta bullo da matakan siyasa don kawo karshen wannan takaddama. (Ibrahim)