Ibrahim Ghandour ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da ya yi tare da takwaransa na kasar Habasha Workneh Gebeyehu, wanda a yanzu haka yake ziyara a birnin Khartoum.
Ibrahim Ghandour ya ce, Sudan a shirye take ta girke sojoji don tinkarar duk wata barazana a fannin tsaro. Sa'an nan a nasa bangaren, Workneh Gebeyehu ya ce, Habasha da Sudan za su karfafa hadin-gwiwa, kana, Habasha za ta dauki matakan da suka dace domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki.
Tuni a ranar 6 ga wata ne, gwamnan jihar Kassala dake gabashin kasar Sudan Adam Jamma ya sanar da rufe bakin iyakokinta da kasar Eritrea tun daga daren ranar 5 ga wata. Har wa yau, Sudan ta kara tura dakarunta zuwa wannan jiha, amma ta musunta cewa, dangantakarta da Eritrea ta yi tsami.(Murtala Zhang)