Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan ta fidda wata sanarwa dake tabbatar da rashin cimma matsaya tsakanin kasar da Masar, game da yankin kan iyakar nan na Halayeb, wanda a yanzu haka ke karkashin ikon Masar.
Tun daga shekarar 1958, a duk shekara Sudan na maimaita korafi ga kwamitin tsaron MDD game da yankin Halayeb, lamarin da take fatan za a warware shi, ko dai ta hanyar tattaunawa da Masar, ko kuma ta shiga tsakani na kasashen duniya.
A shekarar 2016, Masar ta yi watsi da bukatar Khartoum na hawan teburin shawarwari, ko gayyato kasashen duniya domin warware wannan takaddama. A kuma ranar Alhamis din makon jiya, Sudan ta yiwa jakadan ta dake Masar kiranye domin tattaunawa da shi. (Saminu Hassan)