Wata sanarwa da Ministan ma'aikatar Hashim Ali Salem ya fitar jiya ta ce darajar zinaren da ya kai kusan miliyan 400 da kasar ta samu cikin shekarar da ta gabata, ya yi daidai da kudin shigar da kasar ke samu daga man fetur kafin ballewar Sudan ta Kudu.
Hashim Salem ya ce masu hakar ma'adinai na gargajiya ne suka samar da ton 80 na zinaren.
Ya kara da cewa, ma'aikatarsa na aikin cire duk wani shinge dake tarnaki ga zuba jari a bangaren hakar zinari da magance masu fasa kaurin zinare.
Kasar Sudan na duba yiwuwar mayar da zinare babban hanyar samun kudaden ketare bayan ta rasa 3/4 na kudin shigar da take samu daga man fetur saboda ballewar Sudan ta kudu a shekarar 2011. (Fa'iza Mustapha)