Gwamnan jahar Kassala Adam Jamma, shine ya bayar da umarnin rufe dukkan iyakokin kasar da Eritrea, inda ya danganta dalilan da suka sa aka rufe kan iyakar kasar da cewa an kafa dokar ta-baci ne a jahar.
Wannan mataki ya zo ne 'yan sa'o'i bayan da gwamnatin Sudan din ta musanta samun sabani tsakaninta da kasar Eritrea, ya ce an tura dakarun tsaron zuwa jahar Kassala ne saboda dokar ta-bacin da aka kafa da kuma dokar dake da nasaba da hana yaduwar makamai da ababen hawa da basu da lasisi a yankunan, kana da yakar safarar bil adama da mugaggan makamai da sauran haramtattun kayayyaki.
Dubban sojoji masu tallafawa rundunar tsaron kasar Sudan ne aka tura zuwa jahar.
A ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2017, shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya bada umarnin kafa dokar ta-baci a arewacin jahar Kordofan dake yammacin kasar Sudan da jahar Kassala dake gabashin kasar ta Sudan.
Bisa ga wannan umarnin, dokar ta-bacin zata shafe tsawon watannin 6 ne.