Wata sanarwa da wani fitaccen dan Shi'a a fadin kasar Iraq Mohammed al-Rubaie ya fitar a jiya ta bayyana cewa, kawancen dake karkashin jagorancin firaminista Abadi da kawancen siyasa na jam'iyyar 'yan Shi'a dake karkashin jagorancin Hadi al-Ameri sun kulla makamanciyar wannan kawance a wannan rana, inda suka kira ta sunan "kawancen nasarar kasar Iraq".
Rahotanni na cewa, a ranar 15 ga watan Mayun wannan shekarar ce za a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar ta Iraq. (Maryam)