in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta hallaka mutane 5 a arewacin Iraqi
2017-12-25 11:14:15 cri
Kimanin mutane 5 aka kashe ciki har da wani jami'in dan sanda a wani harin sari ka noke da kungiyar IS ta kaddamar a lardin Kirkuk dake arewacin Iraqi.

Majiyar 'yan sandan ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da mayakan na IS suka kafa wata cibiyar binciken ababen hawa ta bogi a kan hanyar data hada garuruwan Ryadh da Hawijah dake kudu maso yammacin lardin Kirkuk, inda suka tsayar da wata mota dake dauke da mutane 5, ciki har da shugaban hukumar 'yan sanda Kanal Fadhel al-Sab'awi, kuma nan take suka harbe mutanen kamar yadda hukumar 'yan sandan lardin Kirkuk ta tabbatar.

Mayakan masu tsattsauran ra'ayi sun tsere daga wajen bayan sun kashe mutanen biyar, majiyar ta kara da cewa, tuni jami'an tsaro suka kaddamar da bincike don zakulo maharan.

Tun a farkon wannan rana, majiyar jami'an tsaro dake makwabtaka da lardin Salahudin ta shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe wasu jami'an tsaro 4 dake aiki da Hashd Shaabi kana an kuma jikkata wasu jami'an 6 a wani hari wanda mayakan IS da yawansu ya zarta 30 suka kaddamar a sansanin jami'an tsaron na Hashd Shaabi dake kusa da garin Dour a gabashin lardin babban birnin Tikrit, mai nisan kilomita 170 a arewacin Baghadaza.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China