in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen kasar Sin ya gana da shugaban kasar Rwanda
2018-01-14 13:09:29 cri

Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin, ya gana da shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, a fadar shugabancinsa dake birnin Kigali, hedkwatar kasar Rwanda, a jiya Asabar.

Yayin ganawarsu, mista Wang Yi ya ce, karkashin jagorancin shugaba Kagame, gwamnatin kasar Rwanda ta samu wata turbar raya kasa da ta dace da yanayin kasar, tare da samun goyon baya daga jama'ar kasar, don haka kasar Sin na son kara mu'amala tare da Rwanda ta fuskar fasahohin gudanar da mulki, tare da neman karfafa amincewar juna a fannin siyasa, da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban, da kara musayar al'adu don zurfafa fahimtar juna, da kyautata fasahar tinkarar al'amuran kasa da kasa da na wasu yankuna. Kana bisa matsayinta na sahihiyar aminiyar kasar Rwanda da ta dukkanin kasashen dake nahiyar Afirka, kasar ta Sin za ta goyi bayan shugaban Kagame a kokarinsa na sauke nauyin dake bisa wuyansa a matsayin shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka AU, da taka rawar gani a fannonin kara hadin kan kasashen Afirka, da daga matsayin nahiyar a idanun duniya.

A nasa bangaren, shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda ya ce, huldar dake tsakanin Rwanda da Sin tana cigaba da samun kyautatuwa. Kasar Rwanda tana yabawa kasar Sin kan irin goyon bayan da take baiwa Rwanda da gudunmowa bisa kokarinta na raya kasa. Shugaban ya kara da cewa, a wannan zamanin da ake ciki, nahiyar Afirka na fuskatar kalukaloli gami da damammakin raya kasa, saboda haka ana fatan ganin kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa ga aikin raya nahiyar Afirka. Kasashen Afirka suna amincewa da kasar Sin, suna kuma fatan karfafa huldar dake tsakaninsu da kasar ta Sin, in ji shugaban Kagame. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China