in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci kasashen Afrika da su janye daga kotun ICC
2017-12-21 10:42:38 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya bukaci kasashen Afrika da su aiwatar da matsayar da aka cimma a taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU, kuma su janye daga zama mamba a kotun hukunta manya laifukan yaki ta kasa da kasa wato (ICC), matukar ta gaza cimma muradun kasashen Afrikar.

Al-Bashir ya bayyana hakan ne a jiya Laraba yayin ganawa da takwaransa na kasar Rwanda Paul Kagame, wanda shi ne shugaban zaman kungiyar ta AU na wannan karo.

Al-Bashir ya fada a lokacin gabatar da jawabi a taron tattaunawar cewa, kasar Sudan tana gayyatar takwarorinta na kasashen Afrika da su aiwatar da matsayar da aka cimma a taron kolin na AU, musamman ma na janyewa daga mamba na kotun ICC, matukar ta gaza daukar matakai na biyan muradun kasashen na Afrika.

Shugaban ya yabawa kasar Rwanda bisa irin matsayinta na nuna goyon bayan Sudan a game da batutuwan kasa da ksa da na shiyya har ma da matsayarta game da batun na ICC.

Kana ya kara yabawa kasar ta Rwanda game da gudumowar da take bayarwa wajen cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar Afrika ta hayar shiga shirin kiyaye zaman lafiya a nahiyar.

A nasa bangaren shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya jaddada aniyar kasarsa na karfafa mu'amala da kasar Sudan a dukkan fannoni don cin moriyar al'ummomin kasashen biyu, kana shugabannin biyu sun sha alwashin hadin gwiwa don amfanawa jama'ar kasashen nasu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China