Baje kolin da aka bude a jiya Alhamis a filin Gikondo na Kigali babban birnin kasar, zai kai har ranar 5 ga wannan watan.
Mashirya taron sun ce manufarsa shi ne, kara wayar da kan jama'a game da abubuwan da ake da su a kasar, wadanda a baya ake shigar da su daga ketare.
An baje kayayyakin da suka hada da na katako da robobi da na fasaha da yaduka da abinci da kayayyakin gona da aka sarrafa da kayayyakin kwalliya na mata wadanda aka yi da hannu da sauran kayayyaki a kan farashi mai rahusa.
Da yake bude taron baje kolin, Ministan ciniki da masana'antu na Rwanda Vincent Munyeshyaka, ya ce taron zai bada dama ta musammam ga kamfanoni cikin gida da kuma daidaikun 'yan kasuwa, wajen nunawa da sayar da kayayyakinsu, tare kuma da samun wata kafa ta tallata kayayyakin.
Wayar da kai domin inganta samar da kayayyki a cikin gida da kuma sayen kayayyakin, zai karfafa gwiwar kirkirar abubuwa da kasuwanci, abun da zai samar da ayyukan yi a Rwanda. (Fa'iza Mustapha)