in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Rwanda ya alkawarta fadada hadin gwiwa da kasar Sin
2017-08-21 10:24:19 cri

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya bayyana aniyar gwamnatin sa ta fadada hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasar Sin, tare da daga matsayin kawancen su zuwa wani sabon mataki.

Shugaba Kagame ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da wakilin musamman na shugaban kasar Sin Liu Xiaofeng, wanda ya halarci bikin rantsuwar shugaban na Rwanda a Kigali fadar mulkin kasar.

Mr. Kagame, wanda ya sha rantsuwar ci gaba da rikon ragamar gwamnatin Rwanda a ranar Jumma'ar da ta gabata, ya godewa shugaba Xi bisa tura wakili don halartar bikin, yana mai fatan Mr. Liu zai isa da sakon godiyar sa ga shugaba Xi.

Ya ce ko shakka babu Rwanda da Sin sun dade suna dasawa, tare da cin gajiyar juna a fannoni daban daban. Kuma Sin ta tallafawa Rwanda da ma wasu karin kasashen Afirka a tsawon lokaci, wajen samar da ci gaba mai dorewa.

A nasa jawabin Mr. Liu Xiaofeng, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin, cewa ya yi tun kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin sassan biyu shekaru 46 da suka gabata, an samu ci gaba mai ma'ana a fannin bunkasa ci gaba cikin daidaito.

Ya ce Sin na fatan hada kai da Rwanda, wajen fadada amincewa juna ta fuskar siyasa da tattalin arziki, da cinikayya, tare da bunkasa kawance tsakanin al'ummun sassan biyu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China