in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya yi hasashen ci gaban tattalin arzikin Rwanda a shekaru masu zuwa
2017-12-21 09:34:32 cri
Wani rahoto da bankin duniya ya wallafa a jiya Laraba, ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Rwanda zai bunkasa da kaso 5.2 cikin 100 daga watan Yuni zuwa na Disamba na shekarar 2017.

Rahoton ya ta'allaka ci gaban ne kan yadda gwamnati da sassan masu zaman kansu ke kara mayar da hankali wajen zuba jari da kuma ci gaban aikin noma a kasar.

Rahoton bankin karo na 11 mai taken "yadda ake fasalin birane a Rwanda, da yadda hakan zai farfado da tattalin arzikin kasar", ya kuma nuna cewa, tattalin arzikin kasar ba zai fuskanci tangarda cikin matsakaicin wa'adi ba, ana kuma sa ran farashin albarkatun kasa da ake fitarwa zuwa ketare, kamar ganyen shayi, da gahawa da musayar kudaden da ake takara, za su farfado

Wata sanarwa da masanin tattalin arziki na bankin Aghassi Mkrtchyan ya fitar a birnin Kigalin kasar ta Rwanda ya bayyana cewa,yadda gwamnati ke zuba jari a wasu fannoni da ake samun riba mai yawa da yadda ake magance matsaloli dake hana ruwa gudu, duk sun taimaka wajen daidaita yanayin da ake ciki a shekarun baya-bayan nan.

Rahoton ya kuma tabbatar da cewa, kasar dake gabashin Afirka tana canjawa cikin sauri, kana karuwar jama'a a biranen kasar ta kara girman biranen, musamman birnin Kigali da sauran manyan biranen dake kewaye.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China