in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu zuba jari na kasar Sin sun nuna sha'awar su ga Rwanda
2015-08-04 09:12:56 cri
Wani gungun Sinawa 'yan kasuwa sun nuna sha'awar shiga hada-hadar zuba jari a kasar Rwanda.

Masu zuba jarin su sama da 30 karkashin jagorancin shugaban cibiyar cinikayyar kasar Sin a gabashin Afirka Han Jun, sun bayyana wannan matsayi na su ne a birnin Kigali, inda suka ce za su duba yiwuwar shiga harkokin gina ababen more rayuwa, da harkar masana'antu, da kuma ta gine-ginen gidaje.

A cewar shugaban tawagar, matakin da cibiyar ta sa za ta dauka zai taimaka wajen janyo hankalin karin Sinawa su zuba jari a Rwanda, da ma sauran sassan yankin na gabashin Afirka.

Da yake maida jawabi yayin ganawar sa da tawagar 'yan kasuwar, shugaban ofishin samar da ci gaba na kasar ta Rwanda Francis Gatare, cewa ya yi tawagar daya ce daga matakan da ake dauka, na janyo Sinawa masu zuba jari kasar ta Rwanda.

A yanzu haka dai yawan jarin da Sinawa masu zuba jari ke da shi a Rwanda cikin shekaru 5 din baya bayan nan, ya haura dalar Amurka miliyan 170. Adadin da ya hada da kudaden cinikayyar shige-da-fice tsakanin kasashen 2. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China