in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin mai kula da aikin yaki da cin hanci da rashawa ya ziyarci Najeriya
2017-09-09 13:33:25 cri
Darektan ofishin sa ido kan ayyukan jami'ai na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mista Li Xiaohong, ya jagoranci wata tawaga domin kai ziyara Najeriya, inda ya gana da ministan shari'a na kasar, Abubakar Malami, da mukadashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Ibrahim Magu, da kuma Gwamnan babban bankin kasar Mr. Godwin Emefiele, inda suka yi musayar ra'ayi kan huldar dake tsakanin kasar Sin da Najeriya, da hadin gwiwar dake tsakaninsu ta fuskar yaki da cin hanci da rashawa.

Li Xiaohong da tawagarsa sun kai wannan ziyara ne tsakanin ranar 6 zuwa 8 ga watan nan da muke ciki.

Yayin ganawarsu, Mista Li ya gabatar da yanayin da ake ciki a kasar Sin a bangaren aikin ladabtar da jami'an kasar, da kuma yaki da cin hanci da rashawa, tun bayan da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta gudanar da babban taronta na 18 a shekarar 2012.

A cewar jami'in na kasar Sin, jam'iyyar Kwaminis da gwamnatin kasar, suna da kudurin kawar da munanan ayyukan cin hanci da rashawa, al'amarin da ya sa su daukar nagartattun matakai tare da cimma nasarori sosai a fanni. Lamarin da ya ce, ya sanya jama'ar kasar Sin nuna amincewa da goyon baya ga jam'iyyar Kwaminis da gwamnatin kasar. Kasar Sin dai, na mai da hankali sosai kan hadin gwiwar da ake yi a fannin yaki da cin hanci da rashawa tsakanin kasashe daban-daban, inda take samun goyon baya daga gamayyar kasa da kasa, ciki har da Najeriya, a fannin tasa keyar jami'an da suka tsere zuwa ketare, da mayar da kudin jama'a da suka wawure. A don haka ne kasar ke son karfafa alaka da hukumomin Najeriya, don zurfafa hadin gwiwa a fannin yaki da cin hanci da rashawa.

A nasu bangaren, Jami'an Najeriya, wadanda suka yabawa kasar Sin kan nasarorin da ta cimma a fannin yaki da cin hanci da rashawa, sun ce aikin yaki da cin hanci da rashawa wani muhimmin bangare ne na manufofin gwamnatin shugaba Buhari, inda kuma ake samun ci gaba tare da gamuwa da wasu matsaloli. Don haka ne a cewarsu, Najeriya ke son koyon fasahohin kasar Sin, da kokarin hadin gwiwa da ita a wannan fanni.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China