in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Sin na hadin gwiwar dakile kwararar hajoji marasa inganci
2017-08-22 09:02:40 cri
Mahukuntan Sin da na tarayyar Najeriya, na daukar matakan dakile kwararar hajoji marasa inganci da ake shigarwa Najeriya.

Shugaban hukumar dake lura da al'amuran cinikayya na kasar Sin a Najeriya ko CCCN a takaice Ye Shuijin, shi ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya.

Mr. Ye ya ce mafi yawan kayayyakin da ake gani marasa inganci ba kaya ne da ake sarrafa su a Sin ba, kuma bisa kokarin da ake yi na raba kasuwannin Najeriya da irin wadannan kayayyaki, hukumar kula da nagartar hajoji ta kasar (SON), na daukar dukkanin matakai da suka wajaba, na raba kasar da kayan jabu.

Jami'in ya kara da cewa, yanzu haka Najeriya na hadin gwiwa da mahukuntan kasar Sin, wajen tabbatar da cewa kayayyaki masu inganci ne kadai ke samun damar shiga Najeriya daga ketare.

Rahotanni dai na cewa tarin hajoji marasa inganci na kwarara kasuwannin Najeriya, ciki hadda karafan gine gine, da kayan laturori, da kayan abinci, da na amfani a gidaje da dai sauran su.

Ko da a bara ma, sai da hukumar SON ta bayyana cewa, kusan kaso 40 bisa dari na kayayyakin laturori da ake shigarwa Najeriya ba su da inganci, wanda hakan ke jefa rayuka, da dukiyoyin 'yan kasar masu amfani da su cikin hadari.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China