in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya ce a karo na karshe zai tsawaita lokacin dage takunkumi kan Iran
2018-01-13 13:51:20 cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya fitar da wata sanarwa jiya Jumma'a, inda ya ce a karo na karshe zai tsawaita wa'adin dage takunkumin da aka garkamawa kasar Iran, kana, ba zai tabbatar da cewa Iran ta cika alkawarinta na aiwatar da yarjejeniyar nukiliyarta ba.

Trump ya ce, akwai kurakurai masu yawa a cikin yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar Iran, inda kuma ya bukaci majalisar dokokin Amurka gami da kasashen Turai su amince da yin garambawul kan wasu bayanan dake kunshe cikin yarjejeniyar, da hana Iran din cigaba da shirinta na makamai masu linzami.

Bayan da Trump ya fitar da wannan sanarwa, a nasa bangaren, ministan harkokin wajen Iran, Mohammad Javad Zarif cewa yayi, sam ba za'a sake yin shawarwari kan yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar Iran ba, kuma ya kamata Amurka ta cika nata alkawarin na aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma.

Jiya Jumma'a kuma, ma'aikatar kudin Amukar ta sanar da sanya takunkumi kan wasu mutane da kungiyoyi guda 14, wadanda suke da alaka da goyon-bayan Iran ta bunkasa makamai.

A watan Yulin shekara ta 2015, kasar Iran da wasu kasashe guda shida, ciki har da Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Rasha, da Sin gami da Jamus, sun cimma wata yarjejeniya kan batun nukiliya na Iran. Bisa yarjejeniyar, Iran ta alkawarta rage shirinta na raya makaman nukiliya, kuma kasashen duniya zasu soke takunkumin da aka sanya mata. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA na sanya ido kan yadda Iran ta aiwatar da wannan yarjejeniya, kuma a sau da dama akwai rahotannin dake tabbatar da cewa, Iran ta aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China