in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaminista Abe da shugaba Trump na Amurka sun amince su kara matsawa koriya ta Arewa lamba
2017-11-06 21:10:54 cri
Firaministan kasar Japan Shinzo Abe, da shugaban Amurka Donald Trump, sun amince su kara matsawa koriya ta Arewa lamba, game da gwajin nukiliyar da take aiwatarwa.

Jagororin kasashen biyu sun bayyana hakan ne a litinin din nan, yayin da Mr. Shinzo Abe da shugaba Trump ke gabatar da wani taron manema labarai na hadin gwiwa, bayan ganawarsu a birnin Tokyo.

Da yake tsokaci game da hakan firaminista Abe, ya ce Japan za ta fadada takunkumin da ta kakabawa Koriya ta arewa.

Wannan ce dai ziyarar shugaban na Amurka ta farko a yankin Asiya, tun bayan rantsuwar kama aiki da ya yi a watan Janairun bana, kuma kasar ta Japan ce zangon sa na farko, a ziyarar da zai gudanar a kasashen nahiyar biyar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China