A wajen sansanin David Camp dake jihar Maryland na kasar Amurka, Trump ya fadawa 'yan jaridu cewa, yana da niyyar zantawa da Kim Jong Un ta waya, amma duk da haka akwai wasu sharudda, kana, Amurka na da tsattsauran ra'ayi kan Koriya ta Arewa.
Tuni a ranar biyar ga wata, ma'aikatar kula da harkokin karfafa hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin Koriya ta Kudu da ta arewa ta ce, Koriya ta Arewa ta yarda da yin shawarwari tsakanin manyan jami'anta da na Koriya ta Kudu a ranar 9 ga wata a yankin bangaren Koriya ta Kudu dake Panmunjon, inda bangarorin biyu za su tattauna kan batun kyautata alaka tsakaninsu, ciki har da halartar gasar wasannin motsa jiki na Olympics a lokacin hunturu wanda za'a yi a Pyeong Chang dake Koriya ta Kudu.(Murtala Zhang)