"Umarnin da na sanyawa hannu a yau zai mayar da hankali ne kan shirin binciken sararin samaniya na Amurka game da binciko wasu sabbin nau'ikan ilmi wanda dan adam zai iya ganowa" in ji shugaba Trump a lokacin da ya sanar a fadar White House.
Trump ya sake kafa hukumar kula da sha'anin binciken sararin samaniyar ne a watan Yuni inda ya damka alhakin tafiyar da hukumar a hannun mataimakinsa Mike Pence.
A shekarar 1989 ne aka kirkiro majalisar a karon farko, a lokacin mulkin tsohon shugaban Amurkar George H.W. Bush amma daga bisani a shekarar 1993 sai hukumar ta durkushe karkashin mulkin tsohon shugaban kasar Bill Clinton. (Ahmad)