An ruwaito Trump yayin zaman MDD, a lokacin da yake tambaya a ranar Alhamis dalilin da ya sa Amurka za ta karbi Karin 'yan cin rani daga kasashen Haiti da wulakantattun kasashe a Afirka, maimakon kasashe kamar Norway. Rahotanni na cewa, Trump dai ya yi watsi da dokar shigi da fice da manyan jam'iyyun siyasu a majalisar dokokin kasar suka gabatar masa.
Mai magana da yawun UNHCHR Rubert Colville ya ce, kalaman shugaban abin kaduwa ne kuma abin kunya. Kalmar da ta dace a yi amfani da ita, ita ce nuna wariyar launin fata. Don haka bai kamata shugaban ya kira kasashen da ma nahiyar da baki dayan al'ummunsu ba fara ne ba a matsayin wulakantattu ba. A saboda haka ba za a lamunci haka ba.