in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin IOC zai kira taron bangarori hudu a ranar 20
2018-01-12 13:10:21 cri

Shugaban kwamitin kula da harkokin wasannin Olympics na IOC Thomas Bach ya sanar a ranar 10 ga wata, cewar za a kira taron bangarori hudu a babbar hedkwatar kwamitin da ke birnin Lausanne na kasar Switzerland don tattauna batun amincewa da kasar Koriya ta Arewa ta shiga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu.

A ranar 9 ga watan ne manyan jami'an kasashen Koriya ta Kudu da ta Arewa suka yi shawarwari a garin Panmunjon da ke kan iyakar kasashen biyu, inda kasar Koriya ta Arewa ta amince ta tura wata tawaga zuwa gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu karo na 23 da za a yi a birnin Pyeongchang na kasar Koriya ta Kudu, bisa shawarar da Koriya ta Kudu ta gabatar ta shigar da Koriya ta Arewa cikin wasannin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China