in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarin share fagen gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu karo na 24
2017-10-10 20:50:23 cri

Yau Talata kungiyar dake jagorantar aikin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu karo na 24 ta bude cikakken taronta karo na 4 a nan Beijing.

A yayin taron, Zhang Gaoli, mataimakin firaministan kasar Sin kuma shugaban kungiyar ya bayyana cewa, dole ne a yayata da raya wasannin lokacin hunturu. Yanzu sassa daban daban na al'ummar kasar Sin suna nuna goyon baya sosai ga wannan gasa. Kana an fara raya harkokin kasuwanni. Ana kuma share fagen ayyukan ba da hidima yadda ya kamata. An fara ayyukan gudanar da filin wasa, sufuri, da samar da wurin kwana da dai sauransu. Har ila yau kwamaitin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu karo na 24 yana ta inganta karfinsa, yana kuma kyautata hadin gwiwa a tsakaninsa da hukumomin wasanni na kasa da kasa, lamarin da ya ba da tabbaci wajen gudanar da ayyukan shiryawa yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China