Da yammacin yau ne aka rufe gasar wasanni ta kasar Sin karo na 13 a dakin wasanni na birnin Tianjin .
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci bikin rufe gasar, inda ya sanar da rufe gasar.
An shafe tsawon kwanaki 12 ana gudanar da gasar wasanni ta kasar Sin karo na 13, inda 'yan wasa fiye da dubu 10 daga tawagogi 38 suka halarci gasar. A wannan karo, an karya matsayin bajimta na duniya guda hudu da na Asiya guda 3. An gudanar da sabbin wasanni 19 da Sinawa daga sassan kasar daban-daban suka halarta, kuma yawan jama'ar da suka halarci wasannin ya zarce miliyan daya, daga cikin masu halarta gasar akwai masu shekaru 4 kawai, kana mafi tsohon shekaru shi ne 93. (Zainab)