Kwanan baya, an kaddamar da sanarwar daukar ma'aikata a shafin internet na kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu na shekarar 2022 na Beijing, hakan da ya kasance karo na farko ne da kwamitin ya dauki ma'aikatansa daga duk fadin duniya.
An labarta cewa, kwamitin ya samar da guraben aikin yi guda 21, tare da daukar ma'aikata 22, a cikinsu kuma wasu 11 na guraben aikin yi guda 10 ne aka nemi dauka daga duk fadin duniya. Wadanda suka gwanance a fannonin tsara fasali, tafiyar da dakin wasannin motsa jiki, raya kasuwa, kafofin yada labaru, harkokin kudi, ilmin shari'a, harsunan waje da dai sauransu za su iya mika takardar neman samun aikin yi.
Kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu na shekarar 2022 na Beijing zai shirya wa masu neman aikin yi wadanda suka dace da bukatu jarrabawa, intabiyu, da duba fayil dinsu. Zai kuma tsai da kuduri na karshe kan wadanda za su samu aikin yi bisa yin la'akari da makin jarrabawarsu, tarihinsu na aiki da kuma yadda suka dace da guraben aikin yi. (Tasallah Yuan)