in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin da takwaransa na kasar Rasha sun taya juna murnar sabuwar shekara ta wayar tarho
2015-12-31 11:36:05 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na kasar Rasha Dmitry Medvejev sun taya juna murnar sabuwar shekara ta wayar tarho.

Inda Li Keqiang ya taya murnar sabuwar shekara ga Dmitry Medvejev, kuma ya bayyana cewa, a daidai lokacin da ake shiga sabuwar shekara, huldar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Rasha bisa manyan tsare-tsare na samun bunkasuwa mai kyau.

Bugu da kari, Li Keqiang ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasashen Sin da Rasha na cikin muhimmin lokacin neman samun bunkasuwa, inda haka yake son rika yin cudanya tare da takwaransa domin karfafa huldar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu da kawo moriyar jama'arsu.

A nashi bangaren Dmitry Medvejev ya bayyana cewa, huldar abokantaka ta gargajiya a tsakanin kasashen Rasha da Sin na samu bunkasuwa mafi kyau a tarihi. A cikin sabuwar shekara, yana son rika tuntubar kasar Sin yadda ya kamata.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China