in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya isa Sochi don halartar taron SCO
2017-11-30 19:42:51 cri
A yau ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya isa birnin Sochin kasar Rasha don halartar taron firaministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai(SCO) karo na 16.

Taron wanda zai gudana daga yau Alhamis zuwa gobe Jumma'a, shi ne irinsa na farko tun bayan da aka fadada wakilcin kungiyar a watan Yunin, inda aka sanya kasashen Indiya da Pakistan.

Kungiyar wadda aka kafa ta a shekarar 2001, tana da mambobin da suka hada da kasashen Sin da Kazakhstan, Kyrgzstan da Rasha, Tajikistan, Uzbekistan. Sauran sun hada da Indiya da kuma Pakistan. Kana akwai kasashe 'yan kallo da suka hada da Afghanistan da Belarus da Mongolia. Sai kuma abokan tattaunawa gida shida, wato Armenia, Azerbaijan da Cambodia, Nepal da Sri Lanka da kuma Turkiya.

Kafin Li Keqiang ya isa birnin Sochi, sai da ya gana da shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha a birnin Moscow a jiya Laraba, inda shugabannin biyu suka amince su karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma hadin gwiwa a dukkan fannoni.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China