in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 3 sun mutu a wani harin da ake zargin Boko Haram da kaddamarwa a Kamaru
2017-12-24 12:41:52 cri

A kalla mutane 3 ne aka hallaka a wasu tagwayen hare hare da ake zargin mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram da kaddamarwa a ranakun Juma'a da Asabar a yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru.

Wata majiya daga kwamitin 'yan sintiri a yankin, ta tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hari na farko ya faru ne da yammacin ranar Juma'a a yankin Mayo-Moskota wanda ke makwabtaka da Najeriya, inda ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne suka shiga garin Zeneme inda suka kashe mutane biyu.

Hari na biyu ya faru ne a garin Kerawa-Mafa dake wannan yanki inda suka kashe mazaunin garin guda daya.

Yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru, yana yawan fuskantar hare hare masu yawa musamman a 'yan kwanakin nan da ake shirin ban kwana da wannan shekara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China