in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun yi nasarar dakile wani hari da Boko Haram suka shirin kaiwa a Maiduguri
2017-12-26 19:30:38 cri

Rahotanni daga Najeriya na cewa, dakarun kasar suna farautar wasu mayakan Boko Haram, bayan dakile wani hari da suka shirya kaiwa a kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Kwamandan dakarun dake yaki da mayakan na Boko Haram a jihar ta Borno Rogers Nicholas wanda ya sanar da hakan, ya ce, sojojin sama da na kasa na farautar mayakan,a lokacin da suka yi yunkurin kai wani hari a garin Maiduguri a ranar Litinin.

Nicholas ya ce, sojoji sun yi nasarar dakile harin da mayakan na Boko Haram suka shirya kaiwa kan wani barikin soja dake Moloi, 'yan kilomitoci daga Maiduguri. Kuma babu wani soja da ya rasa ransa a wannan bata kashi, sai dai an kona musu motoci biyu

Mayakan Boko Haram dai sun kaiwa barikin sojojin hari ne ta hanyar amfani da abubuwan fashewa da bindigogin da aka girke a kan mota, a kokarin da suke na shiga garin Maiduguri domin su saci kayan abinci.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China