in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta alkawarta hada kai da Rasha domin fadada hadin gwiwar yankinsu
2017-11-30 10:26:36 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada matsayin kasar sa na ci gaba da hada kai da Rasha, ta yadda kasashen biyu za su ingiza hadin gwiwa a yankin su, domin samar da ci gaba.

Firaministan na Sin ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da shugaba Vladimir Putin na Rasha a fadar Kremlin. Ya ce, Sin za ta yi aiki tare da Rasha a fannoni daban daban, domin ba da ta su gudummawa ta aiwatar da kudurori na kasa da kasa, tare da karfafa manufofin ci gaban su, ciki hadda masu alaka da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice.

Mr. Li ya kara da cewa, kasashen biyu za su zage damtse, wajen ganin sun tallafi tsare tsare na ci gaban duniya cikin kyakkyawan yanayi. Har ila yau firaministan na Sin ya bayyana cewa, hadin gwiwar sassan biyu a fannin tattalin arziki ya samu tagomashi, yayin da suke dada kaimi wajen raya harkokin cinikayya, da makamashi, da sufurin sama, da na kasa, da fannin samar da ababen more rayuwa.

Sauran sun hada da samar da kayayyakin raya harkar noma, yayin da kuma suke hadin gwiwa a sabbin fannoni na raya tattalin arziki, ta hanyar amfani da na'urori masu kwakwalwa, da fasahohin zamani, da kirkire-kirkire, da fannin raya kanana da matsakaitan masana'antu.

Firaministan kasar ta Sin ya kara da cewa, kasar sa a shirye take ta daidaita manufofin dake kunshe cikin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, tare da tabbatar da nasarar kudurorin hadin gwiwar nahiyoyin Turai da Asiya ko EEU a takaice.

Ya ce, Sin na da burin taka rawar gani a fannin fadada sassan ci gaba na gargajiya, yayin da take lura da tasirin sabbin ci gaban da ake samu a fannoni mabanbanta.

A nasa bangare, shugaba Putin ya ce, hada hadar cinikayya tsakanin Sin da Rasha na ci gaba da bunkasa, kana hadin gwiwa a fannin raya makamashi, da bunkasa fannin sufuri, da noma da sauran sassan kananan sana'o'i na dada fadada.

Ya ce, za su ci gaba da daidaita manufofin su na samar da ci gaba, ta yadda za su ci gajiyar su tare, yayin da shawarar ziri daya da hanya daya, da sauran shirye shirye na samar da ci gaba, ciki hadda na hadin gwiwar Turai da Asiya a fannin raya tattalin arziki, ke ci gaba da ba da gudummawar cimma nasarar hakan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China