A jawabin da ya yi ga taron, Mista Li ya ce, yadda ake samun ci gaba cikin sauri dangane da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen tsakiya da gabashin Turai 16 gami da kasar Sin, ya sheda amfanin manufar da ake bi ta "zama cikin daidaituwa, da tattaunawa, da kokarin amfanawa juna, da bude kofa, da hakuri da bambancin ra'ayi, da kokarin kirkiro sabbin fasahohi", yayin da ake hadin gwiwar.
Firaministan kasar Sin ya kara da cewa, yayin taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 da ya gudana a watan jiya, an jaddada burin kasar Sin na neman samun ci gaba ta hanyar zaman lafiya, da kokarin kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa, da samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin duniya.
A cewar jami'in, ana kokarin hadin gwiwa tsakanin kasashen dake yankin tsakiya da gabashin nahiyar Turai da kasar Sin ne ba domin takara da wasu kasashe na daban ba. Inda ya ce an yi haka ne don tabbatar da moriyar tattalin arziki, gami da raya huldar dake tsakanin bangarorin 2.(Bello Wang)