in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan asusun nazarin kimiyya da fasaha na Sin da ake nema samun iznin budewa ya karu sosai
2017-12-15 11:08:41 cri
A gun taron aikin sarrafa asusun kimiyya da fasaha na kasar Sin da aka gudanar a kwanakin baya, direktan kwamitin asusun kimiyya da fasaha na kasar Sin Yang Wei ya bayyana cewa, a shekarun baya baya nan, yawan asusun nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da ake neman iznin budewa ya karu sosai, kuma da dama daga shugabannin asusun matasa ne.

Yang Wei ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan asusun nazarin kimiyya da fasaha da aka nemi izinin budewa ya karu da kalla kashi 10.43 cikin dari a kowace shekara. Kana shekarun shugabannin asusun ya ragu daga tsakanin 40 da 50 a shekarar 2010, zuwa tsakanin 30 da 45 a halin yanzu.

A wadannan shekaru, kwararru a fannin kimiyya da fasaha matasa ne daga kasashen waje wadanda suka fi son komowa kasar Sin.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China