in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bunkasa ayyukan kimiyyar samar da bayanai daga sararin samaniya a shekarar 2018
2017-12-27 11:04:15 cri
Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin kara azama wajen bincike, da tattara hotunan da ake dauka da na'urorin tauraron dan Adam a sararain samaniya cikin shekarar 2018 dake tafe.

Kaza lika a shekarar mai zuwa, za a shirya harba tauraron dan Adam na Gaofen-7, wanda ke iya samar da hotuna masu inganci na sassan duniya daga sararin samaniya.

Da yake tsokaci game da hakan, darakta a ofishin dake kula da harkokin safiyo da tsara taswira, tare da tattara bayanin kasa ko NASMG a takaice Kuresh Mahsut, ya ce tauraron dan Adam na Gaofen zai rika samar da bayanai na yanayin duniya baki daya a tsawon sa'o'i 24.

Kuresh Mahsut wanda ya jagoranci taron masana game da wannan aiki da ya gudana a ranar Talata, ya ce Sin za ta bunkasa harkokin bincike, da samar da ci gaba na tauraron dan Adam da aka yiwa take da Ziyuan 03 da 04 duka a shekarar dake daf da shigowa.

Ya ce bisa shirin kasar Sin na fadada samar da kayayyakin binciken sararin samaniya na shekarar 2015 zuwa 2025, za a yi amfani da taurarin dan Adam guda 7 ciki hadda Gaofen-7, domin samar da karin bayanai na taswira, da sarrafa kunbuna, da tsara fasalin birane da kauyuka, da kare muhalli tare da samar da bayanai na kandagarkin bala'u.

Har ila yau Sin za ta bunkasa kokarinta, na magance matsaloli da ke aukuwa ba zato ba tsammani ta hanyar fasashohin safiyo, da shata taswira cikin shekaru 3 masu zuwa.

A shekarar ta badi, shirin NASMG zai gudanar da ayyuka daban daban, da suka jibanci tattara bayanan kasa, da safiyo, tare da fitar da rahoton shekara shekara. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China