An dai kammala dukkanin wani gwaji na amfani da rokar, wadda ke amfani da wani nau'i na daskararren makamashi, an kuma shirya amfani da ita wajen harba taurarin dan Adam guda 6 a bana.
Kuaizhou dake nufin jirgi mai sauri a yaren Sinanci, roka ce da aka kera domin harba taurarin dan Adam cikin nasara, ba kuma tare da bata dogon lokaci wajen shirye shirye ba.
An dai takaita yawan kudin da ake bukata wajen amfani da rokar ta Kuaizhou, kasa da makamantanta da ake amfani da su a sauran kasashen duniya. Da yake tabbatar da hakan, wani jami'in hukumar ta CASIC Zhang Di, ya ce rokar na iya harba kumbuna da nauyinsu ya kai tan 78.
A watan Janairun shekara mai shudewa ne dai aka yi amfani da Kuaizhou mai lamba 1A wajen harba taurarin dan Adam 3, aikin da ya kasance hidima ta farko da wannan nau'i na roka ta aiwatar. (Saminu Hassan)