in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu ci gaba a shirinta na magance gurbatar muhalli
2017-12-11 10:29:41 cri

Ministan kare muhalli na kasar Sin Li Ganjie, ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a yakin da take yi da matsalar gurbatar muhalli da samar da iskar da ake shaka mai inganci, da tsabtar ruwan sha da kula da kasar noma.

Gwamnatin tsakiya ta kaddamar da shirin samar da iska mai tsabta na shekaru 5 a shekarar 2013, da nufin inganta yanayin iskar da ake shaka ta hanyar daukar wasu matakai da suka hada da rurrufe wasu masana'antu, da takaita yawan motoci masu fitar da hayaki, da kuma sauya sinadarin kwal don maye gurbinsa da makamashi mai tsabta.

A watanni 11 na farko na shekarar 2017, wanda ita ce shekarar da shirin zai kare, kimanin biranen kasar Sin 338 ne suka sami ragin kashi 20.4 bisa 100 na raguwar hayaki mai gurbata muhalli PM10, idan aka kwatanta da shekarar 2013. Yanayin hayaki mai gurbata muhalli PM2.5 a manyan yankunan kasar uku da suka hada da yankin Beijing-Tianjin-Hebei, yankin Shanghai-Jiangsu-Zhejing da kuma lardin Guangdong sun samu raguwar kashi 38.2 bisa 100, da kashi 31.7 bisa 100 da kuma kashi 25.6 bisa 100, in ji mista Li kamar yadda ya ambata a farkon watan Disamba.

Li ya ce, gwamnatin Sin ita ma ta dauki matakai a sauran bangarori.

A shekarar 2015, kasar Sin ta fitar da tsarinta game da kiyaye ingancin ruwa, da nufin rage sinadaren dake gurbata ruwa, da inganta samar da ruwan sha mai tsabta da kiyaye al'amurran da suka shafi ruwa nan da shekarar 2020.

A shekarar 2016, majalisar gudanarwar kasar Sin ta kaddamar da shirinta na magance gurbatar kasar noma, da nufin inganta yanayin kasa don samar da amfanin gona mai inganci da lafiya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China