'Yan majalisar dokokin sun amince da gagarumin rinjaye inda suka ankarar da gwamnatin kasar don tsawaita wa'adin dokar ta bacin da nufin baiwa 'yan sandan kasar ikon gudanar da binciken kwakwaf na gida gida don zakulo wadanda ake zargi da ayyukan ta'addanci.
Ministan cikin gidan kasar Gerard Collomb, ya fadawa majalisar dokokin kasar cewa, wannan mataki zai taimaka wajen yaki da ta'addanci, don tabbatar da tsaron rayukan al'ummar Faransawa. Ya kara da cewa, batun yanci da tsaro ba sa cin karo da juna. (Ahmad)