in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban majalisar dokokin Sin ya yi shawarwari da takwarorinsa na kasashen arewacin Turai
2018-01-09 10:43:13 cri
Jiya Litinin a nan birnin Beijing, shugaban kwamitin dindindin na majalisar dokokin kasar Sin, Mista Zhang Dejiang, ya yi shawarwari tare da takwarorinsa na wasu kasashen arewacin Turai, da na kasashen dake kewayen tekun Baltic, wadanda suka hada da Finland, da Norway, da Iceland, da Estonia, da Latvia, da Lithuania da ma na Sweden.

Mista Zhang Dejiang ya ce, akwai dadadden zumunci da ingantaccen hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen arewacin Turai, da kasashen dake kewayen tekun Baltic, musamman kasashen dake kokarin shiga cikin ayyukan shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Shugaban kasar Sin Xi Jinping, na maida hankali sosai kan raya huldar abokantaka tare da kasashen arewacin Turai da na kewayen tekun Baltic. Kana Sin na son yin kokari tare da wadannan kasashe, domin kara kyautata dangantakarsu bisa tushen girmama juna da samun fahimtar juna.

A nasu bangaren, shugabannin majalisun dokokin wadannan kasashen Turai sun bayyana farin-cikinsu matuka da samun damar ziyartar kasar Sin, jim kadan bayan da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kammala babban taron wakilanta karo na 19. Sun kuma jinjinawa kasar Sin saboda dimbin nasarorin da ta samu, da kuma babban nauyin da ta dauka a kai. Kasashen arewacin Turai da kasashen dake kewayen tekun Baltic na fatan karfafa hadin-gwiwa da kasar Sin, da kara mu'amala tsakanin hukumomin kafa doka, da tinkarar kalubalen sauyin yanayi da kiyaye muhalli, da kuma sauran wasu fannoni da dama.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China