in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta taimaka wa kasashe masu tasowa ba da horo kan majalisar dokoki
2016-03-22 10:07:57 cri

Kasar Sin ta ce za ta kaddamar da wani shiri da zai horas da 'yan majalisar dokokin wassu kasashen Asiya da Afrika.

Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin, Zhang Dejiang ya sanar da wannan shirin a wata ganawar karya kumallo da shugaban tarayyar 'yan majalisar dokoki na kasa da kasa, Saber Chowdhury, da kuma shugabannin 'yan majalisar dokokin kasashen Zambia, Rwanda, Kenya, Pakistan, Bangladesh da Cambodia a lokacin taron tarayyar 'yan majalisun kasa da kasa karo na 134.

Mr Zhang ya ce, Sin, a matsayinta na kasar ita ma mai tasowa, za ta yi tsayin daka na kare martaban sauran kasashe masu tasowa, tare da ci gaba da fadada hadin gwiwwa na kudu maso kudu.

A ranar Asabar, Zhang Dejiang ya halarci bikin kaddamar da majalisar, daga bisani ya gabatar da jawabin shi kashegari, abin da ya zama karo na farko da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan kasar Sin ya halarci taron.

A cikin jawabin shi, ya ce, Sin a shirye take na ci gaba da tafiyar da irin tsarin damokradiyar ta, kuma cikin nasara ta samu hanyar ci gaban siyasa da ya tabbatar da cewar, za'a iya tafiyar da demokradiya ta hanyoyi da dama.

Fiye da wakilai 670 ne daga majalisun dokokin kasashe sama da 130 da suka hada da shugabannin majalisun 87 da mataimakan shugabannin majalisun suke halartar taron da za'a gama a ranar Laraba.

Mr Zhang har ila yau a wajen taron ya samu kebewa da shugabannin majalisun dokokin kasashen Masar, Afrika ta kudu da Mozambique domin tattauna yadda za'a habaka dangantakar diflomasiya, da kuma ingiza aiwatar da sakamakon taron hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afrika FOCAC da aka yi a birnin Johannesburg a watan Disambar bara.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China